Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP: Labaran Maku ya sha kaye a zaben fitar da gwani a Nasarawa

Tsohon Ministan Yada labarai Labaran Maku ya sha kaye zaben fitar da dan takarar gwamna na Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa inda Yusuf Agabi ya lashe zaben da kuri’a 214, fiye da Maku da ya samu yawan Kuri’u 160.

Tsohon Ministan yada labaran Najeriya Labaran Maku
Tsohon Ministan yada labaran Najeriya Labaran Maku sahararepoters
Talla

Maku wanda ya ajiye mukaminsa na Minista domin neman kujrar gwamna shi ne ya zo a matsayi na biyu a zaben na Jihar Nasarawa yayin da tsohon Gwamnan Jihar Aliyu Akwe Doma ya samu Kuri’u 129, Solomon Ewuga kuma ya samu kuri’u 31, mataimakin gwamnan Jihar Damishi Luka kuma ya samu kuri’a 12.

Aminu Ringim ne ya samu nasara a Jihar Jigawa, a zaben da aka ce Anas Adamu ya janye.

A jihar Akwa Ibom ‘yan takara 21 suka janye bayan korafin cewar gwamnatin Jihar ta bai wa masu zaben toshiyar naira miliyan guda guda inda Udom Emmanuel ya lashe zaben.

A Jihar Delta ma an samu irin wannan zargi na bai wa masu zaben miliyan guda guda amma Sanata Ifeanyi Okowa ya samu nasara.

Sen Ben Ayade ne kuma ya lashe zaben Jihar Cross Rivers kamar yadda Teslim Folarin ya lashe na Jihar Oyo, bayan Alao Akala da sauran ‘yan takaran sun kauracewa zaben.

A Lagos Jimi Agbaje ne ya kada Musliu Obanikoro, tsohon ministan tsaro. A jihar Enugu tarurruka biyu aka gudanar a lokaci guda, inda Sanata Ayogu Eze ya lashe daya taron, Ifeanyi Ugwuanyi ya kuma lashe dayan.

A jihar Niger Umar Nasko ne ya kada mataimakin gwamnan jihar Muas Ibeto da Sanata Nuhu Aliyu wajen. yayin da a jihar Sokoto aka bayyana cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Mukhtar Shagari ya sha kaye.

Gwamnan mai ci Ramalan Yero ya lashe zaben fitar da gwani a Kaduna. Nuhu Ribadu ne ya kuma ya lashe zaben Adamawa.

A jihar Katsina an bayyana Musa Nashuni a matsayin dan takara kodayake an ce akasarin ‘yan takarar duka sun fice daga bagiren da ake zaben bisa zargin yin magudi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.