Isa ga babban shafi
Nijar

An zabi sabon Kakakin Majalisa a Nijar

Majalisar dokokin kasar Jamhuriyyar Nijar ta zabi Amadou Salifou a matsayin sabon Kakakinta don maye gurbin Hama Amadou wanda ya tsere zuwa Faransa saboda badakalar mallakar ‘yaya ba kan ka’ida ba.

Kofar Shiga Majalisar dokokin Nijar
Kofar Shiga Majalisar dokokin Nijar AFP/Sia Kambou
Talla

Salifou ya samu rinjayen kuri’u 71 cikin 113 da ‘Yan Majalisar suka kada. Kodayake akwai wasu da suka fice zauren majalisar.

Salifou wanda dan Jam’iyyar adawa ne ta MNSD Nasara, amma ya dawo yana goyon bayan shugaban kasa Mahammadou Issoufou.

Hama Amadou babban mai adawa da shugaba Issoufou ya fice Nijar ne a watan Agusta bayan majalisa ta amince a kaddamar da bincike akansa game da badakalar mallakar ‘ya'ya ba bisa ka’ida ba.

Hama Amadou ya ce zargin da a ke ma sa yarfe ne na siyasa, kuma ya ce zai iya kare kansa a gaban mahukuntan Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.