Isa ga babban shafi
Sierra Leone

Ebola; Tawagar Majalisar Dinkin Duniya za ta isa Saliyo

Wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya za ta isa kasar Sierra Leone a ranar lahadi mai zuwa domin karfafa wa kasar gwiwa wajen fada da cutar Ebola, wanda kawo yanzu ta yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane a kasar.

Barack Obama da Margareth Chan, daraktar Hukumar Lafiya ta Duniya
Barack Obama da Margareth Chan, daraktar Hukumar Lafiya ta Duniya REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Shugaban kasar Ernest Bai Koroma ya gabatar da jawabi ta faifan bidiyo kai tsaye ga taron zauren Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York inda ya bukaci kasashen duniya su taimaka wa kasar da kuma sauran kasashen yammacin Afirka da ke fama da cutar.

Aikewa da tawagar ta MDD zuwa Saliyo na a matsayin wata alama ta nuna damuwa da kasashen duniya ke yi dangane da cutar da yanzu haka ta kashe kusan mutane dubu uku a kasashen Saliyo, Liberia, Guinea da kuma Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.