Isa ga babban shafi
Najeriya

Ebola; Najeriya ta cire takunkumi a kan jirgin Asky

A Nigeria, Hukumar kula da tashoshin jiragen saman kasar ta dage haramcin da ta yi wa kamfanin jiragen Asky Air da ke kasar Togo, wanda aka dakatar da bayan shigowarsa Najeriya da mutun na farko da ke dauke da cutar Ebola.

Jirgin kamfanin Asky
Jirgin kamfanin Asky
Talla

Mai magana da yawun hukumar zirga-zirgar jiragen saman Najeriya Malam Yakubu Datti, ya shaida wa gidan rediyo Faransa RFI cewa, an cire haramcin ne bayan da kamfanin ya mutunta ka’idojojin sufuri da na kiwon lafiya da aka shata masa kamar dai sauran jiragen da ke shiga kasar.

To sai dai Datti, ya ce yanzu haka suna ci gaba da sanya ido a kan dukkanin jiragen da shiga Najeriya domin tabbatar da cewa sun mutunta ka’idojin kiwon lafiya da tsaro da aka shata masu don hana shiga da masu dauke da cutar Ebola a cikin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.