Isa ga babban shafi
Ebola

Za a killance kasashe uku da ke fama da cutar Ebola

Wakilai daga kasashen yammacin Afirka da na Hukumar Lafiya ta Duniya da suka halarci da taro domin samar da dubarun hana yaduwar cutar Ebola a birnin Conakry, sun amince da yin aiki tare don killace yankin da cutar ta shafa domin hana ta yaduwa zuwa wasu kasashen yankin.

Yaki da cutar Ebola a Afirka ta yamma
Yaki da cutar Ebola a Afirka ta yamma REUTERS/Samaritan's Purse/Handout via Reuters
Talla

A sanrwar bayan taron da suka fitar, mahalarta taron daga kasashen guinea Conakry, Liberia da kuma Sierra Leone, sun amince da yin aiki kafada da kafada akan iyakokinsu, ta hanyar bai wa ‘yan sanda da sojoji damar killace yankunan daka samu bullar cutar wadda kawo yanzu ta kashe mutane fiye da 700 a wadannan kasashe uku kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.