Isa ga babban shafi
Najeriya

Mahara sun kashe mutane 38 a kauyen Dille na jihar Bornon Najeriya

Rahotanni daga Najeriya sun ce akalla mutane 38 ne suka rasa rayukansu sakamakon wasu hare hare da aka kai wa kauyen Dille da ke cikin yankin Askira na jihar Borno a ranar litinin da ta gabata.

'Yan Boko Haram a Najeriya
'Yan Boko Haram a Najeriya Reuters
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya jiyo daga bakin shaidu na cewa, wasu mutane ne masu tarin yawa dauke da makamai a cikin motoci sannan wasu a kan babura suka afka wa kauyen, inda suka kashe jama’a da kona gidaje da kuma wasu wuraren ibada.

Wannan lamari dai ya zo ne a daidai lokacin da wasu rahotanni ke cewa ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Buttuku da ke cikin jihar Adamawa mai makotaka da Borno inda suka kashe mutane da dama kamar dai yadda wani mai suna Micheal Umaru Jar ya tabbatarwa kamfanin na dillancin labaran na Faransa.

Kawo yanzu dai ba wanda ya dauki alhakin kai hare haren, wadanda bisa ga al’ada ake danganta irinsu da kungiyar Boko Haram.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.