Isa ga babban shafi
Libya

Fada a biranen Tripoli da Benghazi na kasar Libya

An ji karar harbe-harbe da manyan bindigogi a kusa da ginin Majalisar Dokokin kasar Libya da ke kudancin birnin Tripoli a yau lahadi, yayin da shaidun gani da ido ke cewa an ga wasu motoci masu sulke na fitowa daga filin sauka da tashin jiragen saman kasar sun nufi inda ake wadannan harbe-harbe.

mutane na tserewa fada a birnin Benghazi na kasar Libya
mutane na tserewa fada a birnin Benghazi na kasar Libya REUTERS/Esam Omran Al-Fetori
Talla

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin fada ke ci gaba da kazanta tsakanin magoya bayan wani janar na sojan kasar mai ritaya da kuma mayakan sa-kai a birnin Benghazi da ke gabashin kasar Libya.

Tuni dai aka tabbatar da cewa fadan na birnin Benghazi ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 75 tare da raunata wasu akalla 140.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.