Isa ga babban shafi
Libya-Mali

Belmokhtar ya boye a Libya-Mali

Wata Majiyar tsaro a kasar Mali tace Kwamandan Mayakan jihadi Mokhtar Belmokhtar da ake nema ruwa a jallo, ya boye a kasar Libya inda ya ke ci gaba da kulla kai hare haren ta’addanci a kasashen yankin Sahel a Afrika.

Mokhtar Belmokhtar Kwamandan mayakan Jihadi a yankin Sahel
Mokhtar Belmokhtar Kwamandan mayakan Jihadi a yankin Sahel REUTERS
Talla

Majiyar ta shaidawa Kamfanin dillacin labaran Faransa cewa ta yi imanin Kwamandan wanda ya jagoranci hari a wata cibiyar gas a Algeria kuma wanda ake zargi an kashe a kasar Mali yana buya ne a cikin kasar Libya.

Majiyar tace suna da shedun da ke tabbatar masu da cewa Mokhtar Belmokhtar yana cikin Libya domin gudun kada a kashe shi ko a cafke shi.

Tuni Jami’an tsaron Najeriya da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suka tabbatar da cewa Belmokhtar yana raye bai mutu ba.

Belmokhtar shi ne aka bayyana a matsayin shugaban kungiyar Al Qaeda reshen Maghreb wanda ya jagoranci karbe ikon arewacin Mali bayan sojoji sun kifar da gwamnatin farar hula.

A watan Disemban bara ne kasar Amurka ta yi tayin bayar da kudi dala Miliyan 5 ga duk wanda ya taimaka da bayanai akan mabuyar Belmokhtar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.