Isa ga babban shafi
Chadi-Mali

An nuna hoton gawar Belmokhtar da dakarun Chadi suka kashe a Mali

Wani wakilin RFI a arewacin Mali ya wallafa Hoton Mokhtar Belmokhtar kwamnan Al Qaeda da aka ruwaito dakarun Chadi sun kashe. Dan Jaridar yace ya samu hoton ne a wayar salula daga hannun Sojan Chadi da ke yaki a Arewacin Mali.

Hoton gawar Belmokhtar da wakilin  RFI ya samu daga hannun dakarun Chadi da suka kashe a arewacin Mali
Hoton gawar Belmokhtar da wakilin RFI ya samu daga hannun dakarun Chadi da suka kashe a arewacin Mali rfi:Madjasra Nako
Talla

A ranar Assabar ne dakarun Chadi suka ce sun kashe Mokhtar Belmokhtar a tsaunin Ifoghas.

Hoton ya nuna Belmokhtar jina-jina wanda ake zargin ya jagoranci ‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da turawa 37 a Algeria.

Rahotannin kisan kwamandojin Al Qaeda  ya ja hankalin kasashen Duniya.

A ranar Litinin ne Shugaban Chadi Idriss Deby Itno ya tabatar da cewa dakarun kasar shi sun kashe Belmokhtar da kuma kwamandan Al Qaeda Abou Zeid.

Rahotanni sun ce Belmokhtar dan asalin kasar Algeria ne wanda ya balle daga kungiyar Al Qaeda reshen Maghreb bayan ya kafa kungiyar shi ta kishin Islama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.