Shirin al'adunmu na Gado yau ya tafi kasar Sudan ne inda muka tarar da wata Kabila da ake kira Hadan Dawa. Wannan Kabilar dai a bisa al'adarsu, basa Wanka duk yanda za'ayi kuwa sai dai in Ruwan Damina ya doki mutum amma tsakaninsu da Ruwa sai sha da sauran mu'amala.
Wani abin al'ajabi ga wannan kabilar shi ne mutum ba zai bayyana Son da yake yiwa Mace ba duk yanda yake bukatar Aurenta, in kuwa ya kuskura ya fada to Mahaifinta ka iya kashe shi domin ya keta Hakkin kallon Fuskar 'yarsa, ba tare da ya bashi 'yancin yin hakan ba.
Wakilin mu a Sudan Mannir Sani Fura-girke ya yi mana nazari akan wannan kabilar a cikin shirin al'adunmu na Gado da Faruk Muhammad Yabo ke gabatarwa a kowane Mako.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu