Isa ga babban shafi
Sudan-Sudan ta Kudu

MDD ta bayyana matsalar da ke hana ayyukan kare fararen Hula a Darfur

Majalisar dunkin Duniya ta ce matsin lambar da hukumomin kasar Sudan suka yi, da rashin kayan aiki na kawo tsaiko a ayyukan wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur. Wadannan matsalolin na hana wa dakarun majalisar ta Dinkin Duniya su kare fafaren hula da ma masu aikin agajin

Darfur
Darfur Reuters
Talla

Sakatare janar na Majalisra dunkin Duniya Ban Ki Moon ne, ya bayyana matsan lambar da Dakarun majalisar ke fuskanta, a lokacin da yake bitar ayyun Twaggar Dakarun wanzar da zaman lafiya ta UNAMID, da ke aiki a karkashin amincewar kwamitin tsaro na Majalisar da dunkin Duniya.

Tawaggar ta UNAMID mai shekaru 6, da keda jami’ai kusan dubu 20, da suka hada da Soji da ‘yan sanda na daya daga cikin rudunonin zaman lafiyan da suka fi girma a Duniya.

Sauyin da ake samu, kan yakin na Darfur, da aka shafe shekaru 11 ana gwabazawa tsakanin sojin gwamnati da ‘yan tawaye, ya sa Majalisar dunkin Duniyar ta fara nazarin ayyukan rundunar.

Sau da dama dai ana farwa su kansu Dakarun na UNAMID, don ko a shekarar da ta gabata ta 2013 kawai an kai musu hari har sau 19, inda mutane 16 suka mutu, 27 kuma suka sami munanan raunuka.

Haka ma an lalata motoci da makamai da sauran kayan aiki.
Majalisar ta dunkin duniya ta ce a shekarar da ta gabata, mutane dubu 380 suka rasa gidajensu a yankin Darfur, alkaluman da suka fi kowanne yawa tun cikin shekarar 2004.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.