Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya za ta bi salon lalama wajen yaki da ta’addanci

Mai bai wa Shugaban kasa Shawara kan sha’anin tsaro Sambo Dasuki ya fito da wani sabon tsari na bin hanyoyin lalama wajen yaki da kungiyar Boko Haram da hare haren ta’addanci da suka yi sanadin mutuwar dubban mutane a Najeriya.

Wani hari da Mayakan Boko Haram suka kai a garin Kawuri, Jahar Borno
Wani hari da Mayakan Boko Haram suka kai a garin Kawuri, Jahar Borno REUTERS/Stringer
Talla

Wasu daga cikin tsarin da za’a bi sun kunshi inganta rayuwa tare da gyra halayen mayakan da ake tsare da su a cikin gidajen yari tare da horas da Jami’an gidan yarin ta bangaren ilimin sanin dabi’un dan adam.

Kuma Ofishin Sambo Dasuki yace zasu hada hannu da shugabannin al’umma da kungiyoyin fararen hula domin kula da yadda ake aiwatar da shirin.

Dasuki yace ya zama wajibi su dauki wannan sabbin matakan saboda girman akidar kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabaci tare da fadakar da al’umma haramcin ta’addanci ga addinin Islama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.