Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: An bude taron kasa a Abuja

Shugaba Goodluck Jonathan ya kaddamar da taron tattauna makomar Najeriya a birnin Abuja a wannan lokaci da kasar ke fuskantar matsalolin tsaro da kabilanci da addini. Wakilai kusan 500 aka zabo daga sassan kasar daban daban a taron wanda ya ke ci gaba da haifar da cece-kuce akan muhimmacinsa.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan Reuters/Tiksa Negeri/Files
Talla

Manyan batutuwan da ake ganin zasu mamaye zaman taron sun hada da hare haren ‘Yan bindiga da mayakan Boko Haram da matsalar cin hanci da rashawa.

Shugaba Jonathan ya ba dukkanin wakilan kasar damar su fito da batutuwan da suke ganin sun shafi ci gaban kasa amma ba tare da tabo batun raba Najeriya gida biyu ba.

Sai dai kuma a sharhin Jaridun Najeriya suna ganin batun raba kasa yana cikin ajandar mahalarta taron.

Taron na tattauna makomar Najeriya na zuwa ne bayan an yi bikin cika shekaru 100 da dunkulewar yankin arewaci da kudanci a matsayin kasa “Najeriya”.

Najeriya mai arzikn Fetir a Afrika, amma har yanzu al’ummar kasa na fama da talauci da matsaloli da dama da suka shafi ci gaban kasa.

Babban kalubalen Najeriya yanzu shi ne matsalar tsaro musamman a wasu yankunan arewacin kasar da ke fuskantar hare haren Mayakan Boko Haram.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.