Isa ga babban shafi
Uganda

Ladar dala milyan 5 ga wanda ya taimaka da labarin kama Joseph Kony

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Amurkar ta fitar, ta bayyana cewa shugaban na kungiyar ta LRA Joseph Konny na matsayin mutumin da take nema ruwa a jallo domin kasantuwarsa wanda ya aikata miyagun laifuka mafi muni a cikin kasarsa ta Uganda, da sauran kasashen yankin Taskiya da kuma gabacin Afirka.

Talla

Joseph Kony wanda ake kyautata zaton cewa yanzu haka yana boye ne ko dai a jamhuriyar Tsakiyar Afirka, ko Sudan ko kuma Sudan ta kudu, Amurka da sauran kasashen yankin sun jima suna farautarsa domin cafke shi, to amma dai har yanzu ba su kai ga samun nasara ba.
Ko baya ga Amurka da kuma gwamnatin kasarsa ta asali wato Uganda, hatta ma kotun kasa da kasa mai hukunta laifukan yaki na neman shugaban kungiyar LRA domin canjinsa da laifufuka da suka hada da na yaki, yi wa mata fyade, kirewa jama’a gabobi, kisan gilla da kuma daukar yara kanana aikin soja.
Yanzu haka dai akwai sojojin kasar Amurka fiye da 100 da ke gudanar da abin da suka kira aikin farautar wannan dan tawaye, wanda aka bayyana shi a matsayin daya daga cikin mutanen da suka fi cutar jama’a a tarihin tawayen Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.