Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyar Boko Haram ta yi barazanar kai sabbin hare-hare

Rahotanni daga Najeriya sun ce, kungiyar Jama’atu Ahlul Sunnah lida da’awati wal jihad, da ake kira Boko Haram, ta yi barazanar kai hari kan Sarakuna, jami’an gwamnati da kuma shugabanin Arewacin kasar.

Imam Abubakar Shekau, na kungiyar Jama'atul Ahlil Sunnah Lidda'awati Wal Jihad
Imam Abubakar Shekau, na kungiyar Jama'atul Ahlil Sunnah Lidda'awati Wal Jihad
Talla

Wani sako da aka ruwaito shugabanta, Abubakar Shekau ke bayani, ya zargi wadanna shugabani da hada baki da jami’an tsaro ana kai musu hari, inda ya musanta rahotan tattaunawa da gwamnati, kana kuma yayi korafi kan yadda jami’an tsaro ke kama matansu.

Kana kuma yayi Allah wadai da fim din da akayi a Amurka, wanda ya ci zarafin addinin Islama.

Shugaban kungiyar kuma ya tabbatar da cewa babu abin daya same shi, inda ya kara da cewa, yana nan lafiyarsa lau.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.