Isa ga babban shafi
Colombia-Cuba

'Yan tawayen FARC sun sace wasu jami'an gwamnatin Colombia

‘Yan tawayen FARC na kasar Colombiya sun sanar da kama wasu jami’an gwamnatin kasar uku da suka hada da wani janar din sojin kasar, bayan da suka shiga wani yankin dake karkashin yan tawayen. Wanan kamen na zuwa ne a dai dai lokacin da ake gudanar da tattaunawa tsakani ‘yan tawayen da Gwamnatin Colombia. Ana dai tattaunawar ne a kasar Cuba.Sace wadanan mutane ya janyo dakatar da tattaunawa da dama ake yi tsakani Gwamnatin da wadanan ‘yan tawaye.Sanarawar da shugaban Kasar Juan Manuel Santos ya fitar ta bayana matukar baci ran shugaban, kan abinda ya kira zagon kasa daga ‘yan tawayen na FARC, a dai dai lokacin da ake gudanar da tattaunawar kawo karshen yakin tsakani bangarorin biyu da aka jima ana gwabzawa.A farkon soma wadanan tattaunawa a kasar Cuba kasashe da dama ne suka bayana farin cikin su, tareda nuna cikkaken goyan baya kan wanan sabuwar manifa ta cima zaman lafiya a kasar.Duk da wannan sai ga shi a safiya jiya Talata ‘yan tawayen sun sanar da yin garkuwa da wasu sojan kasar Colombia uku, al’amarin da ya haifar da cecce kuce, tare da sanar da yin watsi da zaman tattaunawa daga bangaren Gwamnatin Colombiya. 

Bajen 'yan tawayen FARC na Colombia
Bajen 'yan tawayen FARC na Colombia MrPenguin20/wikimedia.org
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.