Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan ya kai ziyarar bazata a Baga da Mubi

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kai ziyara garin Baga da Mubi bayan Sojin kasar sun kwato garuruwan daga hannun Mayakan Boko Haram da suka kashe mutane da dama. Shugaban ya ce ya kai ziyarar ne don ganewa idonsa tare da jajantawa mutanen yankin.

Hoton tauraron Dan Adam da ke nuna ta'adin da Boko Haram ta yi a Baga da Doron Baga
Hoton tauraron Dan Adam da ke nuna ta'adin da Boko Haram ta yi a Baga da Doron Baga
Talla

Jonathan ya fara kai ziyara ne a garin Mubi a Jihar Adamawa kafin ya tafi Baga a Jihar Borno inda Mayakan Boko Haram suka kona tare da kashe mutane sama da 150.

Shugaban ya jinjinawa Sojojin kasar akan kokarin da suke tare da yin alkawalin ba su kyauta idan sun kakkabe Boko Haram.

Ziyarar shugaban na zuwa ne bayan babban hafsan sojan kasar Janar Kenneth Minimah ya kai ziyara a Baga a ranar Laraba, inda ya shaidawa dakarun kasar cewa yaki da Boko Haram ya kusan kawo wa karshe.

Rundunar Sojin tace tana samun gagarumar nasara a yakin da ta ke da kungiyar Boko Haram yanzu haka.

Shugaba Jonathan dai ya sha suka kan rashin daukar matakan da suka dace domin kawo karshen Boko Haram da suka kashe mutane sama da 15,000.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.