Isa ga babban shafi
Wasan Tennis

Nadal da Federer da Sharapova za su kara a gasar French Open bayan daukewar ruwan sama

A fagen gasar Rolland Garros ko kuma French Open da ake bugawa a kasar ta Faransa, a yau ne za a koma buga wasanni manya guda uku bayan ruwan sama da aka tafka a jiya kamar da bakin kwarya ya sa an jingine wasannin.

Rafael Nadal
Rafael Nadal Reuters
Talla

Da farko dai Rafael Nadal dan kasar Spain, wanda ke rike da kofin gasar a bangaren maza zai koma bugawa tsakaninsa da Martin Klazan dan kasar Slovakia.

Ita kuwa Maria Sharapova, 'yar kasar Rasha, wacce ita ke rike da kofin gasar a bangaren mata za ta ci gaba da karawa da Eugenie Bourchard ‘yar kasar Canada a yau bayan ruwa ya sa an tsayar da wasan a lokacin Sharapova tana samun nasara da ci 6-4, 4-2.

Shi kuwa Roger Federer, dan kasar Switzerland zai karasa karawarsa ne da Juliene Benneteau dan kasar Faransa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.