Yankin Hausawa (clone of Afrika

Syndicate contentYANKIN HAUSAWA
Francois Bocande Tsohon Dan wasan Senegal wanda ya mutu yana da shekaru 54
16/05/2012 - Senegal

Dubban mutanen Senegal sun karrama Bocande

A kasar Senegal daruruwan mutane ne suka yi gangami a babban filin wasan kwallon kafa a Dakar, domin karrama fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar Francois Bocande wanda ya mutu a ranar 7 ga watan Mayu a kasar Faransa.

Gungun mata da Amaren da aka daurawa aure a Kano
16/05/2012 - Najeriya

Hisbah ta daura auren Zawarawa 100 a Kano

Hukumar Hisbah a Jihar Kano, ta daura wa Zawarawa 100 aure cikin 1,000 da aka shirya yi, dan magance mace macen aure a Jahar.

kamfanin Areva, mallakar kasar Faransa, da ke hako ma’adinin uranium a Yankin Arlit a Jamhuriyyar Nijar
15/05/2012 - Nijar-Faransa

Wata kungiyar Farin kaya ta nemi kamfani Areva ya biya ‘Yan Nijar diyya

Wata Kungiyar fararen hula a Jamhuriyar Nijar, ta bukaci kamfanin Areva, mallakar kasar Faransa, da ke hako ma’adinin uranium a kasar, biyan kudaden Diyya ga ‘Yan Nijar dai dai da yadda Kamfanin ke biyan Faransawan da suka mutu.

Taswirar kasar Guinea Bissau da kasashen da ke makwabtaka da kasar
15/05/2012 - ECOWAS-Guinea Bissau-Najeriya

Najeriya zata tura dakarunta zuwa Guinea Bissau

Gwamnatin Najeriya tace zata girke dakarunta a kasar Guinea Bissau don taimakawa kasar komawa ga mulkin fararen hula, kamar yadda kungiyar ECOWAS ta bukata.

Taron shugabannin kasashen Kungiyar ECOWAS bayan kammala taro a Dakar kasar Senegal game da rikicin siyasar Mali da Guine Bissau
14/05/2012 - ECOWAS-Mali-Guinea Bissau

Hafsoshin Sojin ECOWAS zasu gana a Najeriya game da Guinea Bissau da Mali

A Yau Litinin ne Manyan Hafsoshin sojin kasashen Afrika ta Yamma zasu gudanar da wani taro a Abuja babban birnin Najeriya, don nazarin hanyoyin da zasu bi wajen girke dakaru a kasar Guinea Bissau da Mali.

Garken Rakuma suna sha ruwa a gabar Tabkin Chadi da ke kewaye da tsaunuka
09/05/2012 - Nijar-Najeriya-Chadi

Kasashen raya tabkin Chadi zasu samar da dakarun hadin gwiwa don yaki da Ta’addanci

Manyan Jami’an tsaron kasashen da ke raya tafkin Chadi, sun gudanar da taro a Jamhuriyar Nijar, don nazarin hanyoyin da zasu dakile safarar makamai da kuma ayyukan ta’adanci domin samun ci gaban kasashensu.

'Yan tawayen Libya rike da muggan makamai a lokacin yaki da dakarun Marigayi Gaddafi
09/05/2012 - Libya

An yi musayar Albarussai tsakanin ‘Yan bindiga da jami’an tsaron Libya

A kasar Libya mutane da dama sun samu rauni tare da samun mutuwar mutum daya sakamakon musayar wuta da aka yi tsakanin Jami’an tsaro da ‘Yan bindiga dwadanda suka yi zanga zanga a Hedikwatar Gwamnati a Birnin Tripoli.

Matan kasar Afghanistan a lokacin gudanar da bukin ranar mata a yankin Ghazni a ranar 8 ga watan Maris
08/05/2012 - Lafiya

Kasar Norway ne iyaye mata suka fi shan dadi amma a Nijar suka fi shan wahala

A wani sabon Rahoto game da halin rayuwar iyaye mata da hukumar kare lafiyar kananan yara ta fitar, ya nuna Nijar ce kasar da iyaye Mata ke shan wahala bayan maye gurbin kasar Afghanistan a karon farko. Kasar Norway ce a matsayin kasa ta farko da iyaye Mata ke shan dadi a jerin kasashe 165 da aka kwatanta rayuwarsu.

Likitocin Najeriya a Jahar Legas lokacin da suke maci domin neman biyansu kudaden Albashi
08/05/2012 - Najeriya

Gwamnatin Jahar Legas a Najeriya ta kori Likitoci 788

Hukumomin Jahar Legas a Najeriya sun tabbatar da sallamar Likitoci 788 wadanda ke yajin aiki tsawon makwanni uku. Gwamnatin Jahar Legas tace yajin aikin Likitocin ya sabawa doka.

'Yan Acaba a Najeriya
07/05/2012 - Najeriya

Gwamnatin Flato a Najeriya ta haramta yin Acaba

Gwamnatin Jahar Flato a Najeriya ta sanar da haramta yin Acaba da babura a birnin Jos da kewaye, saboda yunkurin dakile ayyukan laifi da ake da baburan, kamar yadda ta sanar bayan taron Majalisar ...

Taron Wakilan kasashen ECOWAS a lokacin da suke  tattaunawa akan Guinée-Bissau da  Mali Abidjan, le 26 avril 2012.
03/05/2012 - ECOWAS-Mali-Guinea Bissau

ECOWAS zata tattauna akan batun Guinea Bissau da Mali

A Yau Alhamis ne Shugabanin kungiyar kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, zasu gudanar da wani taro na musamman don tattauna halin da ake ciki a kasashen Gunea Bisau da Mali.

Harin Ginin Kamfanin Jaridar thisday a Abuja Najeriya bayan kai hari
02/05/2012 - Najeriya

Harin This Day: Boko Haram ta yi gargadin sake kai wa kafafen yada labarai hari

Kungiyar Jama'atu Ahlus Sunnah Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da sunan Boko Haram a Najeriya, ta fitar da Wani hoton Bidiyo mai dauke da bayanin harin Ofishin Jaridar This Day tare da yin barazanar ci gaba da kai wasu hare hare a manyan kafafen yada labarai da ma'aikatansu a kasar.

Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Iman Abubakar Shekau a sakonsa ga shugaba Jonathan.
01/05/2012 - Chad-Najeriya

Gwamnatin Chadi ta nemi samar da dakarun hadin kai don yaki da Boko Haram

Gwamnatin kasar Chadi ta yi kiran kasashen 16 a kungiyar raya tafkin Chadi domin samar da dakarun hadin kai don yaki da ‘Yan kungiyar Boko Haram da ke barazana ga sha'anin tsaro a Najeriya da makwabtanta.

Wani Allo dauke da zanen Nicolas Sarkozy da Jam'iyyarsa a lokacin da ma'aikata suka fito zanga-zanga a birnin Lyon na Faransa
01/05/2012 - Duniya

Ranar Ma’aikata: zanga zanga ta barke a wasu kasashen duniya

Kungiyoyin kwadago a kasashen Turai sun shirya gudanar da zanga-zangar adawa da matakan tsuke bakin aljuhun gwamnati domin gudanar da hutunsu na ma’aikata. Ma’aikata a Spain sun shiga zangar zangar ne saboda matsalar rashin aikin yi.

Wasu motocin yakin Jami'an tsaro a Najeriya da aka gani a harabar Jami'ar Bayero a Kano bayan 'Yan bindiga sun kai hari inda suka kashe mutane 20
01/05/2012 - Najeriya

An kwana ana musayar albarussai a Kano tsakanin Jami'an tsaro da 'Yan Boko Haram

A birnin Kano a Najeriya an kwashe daren jiya ana musayar Al barussai tsakanin Jami’an tsaro da wasu da ake zargin ‘Yan kungiyar Boko Haram ne.

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al Bashir
30/04/2012 - Sudan-Sudan ta Kudu

Sudan zata kori ‘Yan kudancin Sudan 12,000

Gwamnatin Sudan ta bada wa’adin mako daya ga ‘Yan kudancin Sudan 12,000 domin  ficewa daga kasar Tare da kafa dokar hana fita akan iyakokin kasashen Biyu. A yau Litinin ne Majalisar Sudan zata yi muhawara akan kudirin dokar katse hulda da Sudan ta Kudu.

lokacin da ake kokarin saka gawawwakin wadanda suka mutu a cikin Mota da kuma wadanda suka samu rauni a harin Jami'ar Bayero a Kano
30/04/2012 - Najeriya

Kiristoci ba zasu mayar da martani ba, amma Gwamnatin Najeriya tace zata sake tattaunawa da Boko Haram

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Namadi Sambo, ya yi kiran Kungiyar Boko Haram ta fito domin amincewa da tattaunawa don samun zaman lafiya a Najeriya, bayan wasu ‘Yan bindiga sun bindige mutane 20 a wajen Ibadar al’ummar Kirista a Jami’ar Bayero a Kano. Amma bayan kai harin Shugaban Kiristocin Jahar Kano Mista Ransom Bello, yace sun la’anci harin amma ba zasu mayar da martani ba.

Harin Ginin Kamfanin Jaridar this Day a Abuja Najeriya
26/04/2012 - Najeriya

Bama bamai sun tashi a Kaduna da Abuja a ginin Jaridar This Day

An samu tashin bom a ginin Kamfanin Jaridar This Day a birnin Abuja bayan wani Bom ya tashi a Kaduna kusa da Ofishin Jaridar a kan titin Kontagora. Jami’an tsaro sun ce an cafke wani mutum da ake zargin ya dala Bom a Kaduna.

Wasu 'Yan Najeriya a lokacin Zanga Zangar adawa da Janye Tallafin Mai
25/04/2012 - Najeriya

Majalisar Wakilan Najeriya ta yi kiran hukunta barayin tallafin Mai

Kwamitin Lawan Faruk mai binciken badakalar bangaren Man fetir a Najeriya yace an sace kudade Dalar Amurka Biliyan Shida daga kudaden Tallafin Gwamnati a shekarun da suka gabata. Majalisar Wakilan Najeriya ta nuna bacin ranta kan yadda wasu jami’an Gwamnati da kamfanoni suke rub da ciki da dukiyar kasa da sunan tallafin man fetur.

Dakarun Sudan ta Kudu rike da Makamai suna iho a sansaninsu da ke yankin Bentiu
23/04/2012 - Sudan-Sudan ta Kudu

Mutane 1,000 suka mutu a rikicin Sudan da Sudan ta Kudu a Heglig

Kwamandan dakarun Sudan yace sama da dakarun Sudan ta Kudu 1,000 ne suka mutu a lokacin yakin da sudan ta kaddamar a yankin Heglig mai arzikin Mai. Kamal Marouf yace Dakarun SPLM 1,200 dakarun Sudan suka kashe kafin su fice daga yankin a ranar Lahadi.

Close