Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

'Wasan Arsenal da Chelsea bai burge ba'

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya yi watsi da koken da wasu masoya kwallon kafa ke yi kan cewa wasan da suka buga da Arsenal da aka dade ana jiran kallo ba ta burge ba musamman saboda an tashi wasan babu ci.

Mourinho na Chelsea
Mourinho na Chelsea REUTERS/Christian Hartmann
Talla

‘yan kallo musamman daga bangaren Arsenal ba su ji dadin yadda ‘yan wasan Chelsea suka taka leda ba.

Tun a filin Emirate gidan Arsenal da aka buga wasan ‘yan kallo ke ta shelar wasan bai burge ba.

Chelsea ce dai ke jagorancin teburin Firimiya, yayin da Arsneal ke bi mata a matsayi na biyu, amma dukkaninsu a sun tsira ne da maki guda, ko da ya ke makin da Chelsea ta samu ya kara ba ta damar lashe kofin Firimiya da wuri.

Amma a lokacin da ya ke mayar da martani Mourinho ya ce ba yawan kwallaye ba ne ke sa wasa ya burge.

‘Ashe da sauran kungiyoyin Firimiya 18 haka suke taka kwallo’.

Mourinho ya ce a a halin da ake ciki a yanzu a Firimiya babu kungiyar da ta fi Chelsea yawan maki, sannan babu kungiyar da ta fi su yawan samun nasara, akan haka ne ma yanzu suke jagorantar teburin gasar gasar.

Tazarar maki 10 ne dai Chelsea ta ba Arsenal da Manchester City yayin da saura wasanni 5 a kammala Firimiya.

Chelsesa dai na iya bikin lashe kofi a karshen mako mai zuwa Idan har ta doke Leicester City a jibi Laraba tare da doke Crystal Palace a Stamford Bridge a ranar Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.