Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

An hada Barca da Bayern, Juve da Madrid

Barcelona za ta kara da Bayern Munich a zagayen dab da na karshe a gasar zakarun Turai, yayin da Juventus za ta fafata da Real Madrid mai rike da kofin gasar bayan an hada kungiyoyin a yau Juma'a a hedikwatar hukumar kwallon Turai UEFA a birnin Nyon.

Barcelona za ta hadu da Bayern Munich, Juventus da Real Madrid a zagayen dab da na karshe a gasar zakarun Turai
Barcelona za ta hadu da Bayern Munich, Juventus da Real Madrid a zagayen dab da na karshe a gasar zakarun Turai UEFA
Talla

Barcelona ce za ta fara karbar bakuncin Bayern Munich a Nou Camp inda tsohon kocin kungiyar Pep Guardiola zai hadu da ‘yan wasan shi.

Barcelona da Bayern sun taba haduwa shekaru biyu da suka gabata a zamanin Tito Vilanova inda Barcelona ta sha kashi da jimillar kwallaye 7 da 0.

A daya bangaren kuma Real Madrid ce za ta fara kai wa juventus ziyara a yayin da za su maimaita tarihi a wasan karshe da suka fafata a 1998, inda Madrid ta lashe wasan da ci 1 da 0 a Amsterdam.

Wannan ne dai karon farko da Juventus ta tsallake zuwa zagayen dab da na karshe bayan shafe shekaru sama da 10, tun a 2003.

Tun kafin a hada kungiyoyin da zasu kara, Shugaban Juventus Giuseppe Marotta ya bayyana cewa za su dogara da sa’a domin tsallakewa zuwa zagayen karshe.

Real Madrid dai na neman kare kambunta ne bayan ta lashe kofin gasar karo na 10 a bara, sai dai kuma a tarihin gasar babu kungiyar da ta lashe kofin sau biyu a jere da jere. Wata kila a bana Carlo Ancelotti zai kafa wa kungiyar tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.