Yarima charles ya kai wa Muhammad Ali ziyara
Tsohon Zakaran Damben Duniya Muhammad Ali ya bayyana Yarima Charls na kasar Ingila a matsayin mutum mafi kima a Idonsa, bayan da Yarima Charles ya kai masa ziyara ta musamman har Garinsu bisa ba zata, a wata ziyarar da Yariman ya kai a kasar Amurka
Wallafawa ranar:
Yarima charles wanda ke tare da rakiyar Matarsa Camila ya sauka a birnin Kentucky na Louisville inda ya nuna matukar sha’awarsa da ayyukan Gona.
Muhammad Ali dai ya rubuta Wasika ne zuwa ga yarima Charles, wadda aka karantawa Yariman a lokacin ziyarar, inda yake bayyana xiyarar tasa a matsayin muhimmiya a wurin shi.
Muhammad Ali mai shekaru 73 dai tsohon Zakaran damben Duniya ne da kuma yayi suna a zamanin da yake wasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu