Isa ga babban shafi
Champions League

Barca ta doke City

Barcelona ta doke Manchester City ci 2 da 1 a karawa ta farko da suka fafata a Etihad a gasar zakarun Turai kafin su sake kece raini a gidan Barcelona. Tsohon dan wasan Liverpool Luis Suarez ne ya jefa wa Barcelona dukkanin kwallayenta biyu a ragar City kafin aje hutun rabin lokaci.

Lionel Messi yana fafatawa da Vincent Kompany na Manchester City.
Lionel Messi yana fafatawa da Vincent Kompany na Manchester City. Reuters / Jason Cairnduff
Talla

Wannan ne karo na farko da Luis Suarez ya kawo ziyara Ingila bayan ya koma Barcelona daga Liverpool a bara.

Sergio Aguero ne ya ramawa wa City kwallon guda a ragar Barcelona.

Messi ya barar wa Barcelona da Fanariti ana dab da kammala wasa.

An kammala wasan ne kuma City na da ‘yan wasa 10 bayan alkalin wasa ya ba Clichy jan kati.

Duk da kashin da ya sha a hannun Barcelona amma kocin City Manuel Pellegrini ya ce za su yi kokarin shiga filin Barcelona su samu nasara a karawa ta biyu.

A daya bangaren kuma Juventus ta doke Borussia Dortmund 2 da 1, a karon farko da kungiyoyin suka hadu tun shekarun 1997 da Dortmund ta doke Juve a wasan karshe.

Carlos Tevez da Morata ne suka jefa wa Juventus kwallayenta a ragar Dortmund.

A yau Laraba kuma Arsenal za ta karbi bakuncin Monaco ne a Emirate, inda Arsene Wenger zai hadu da tsohuwar kungiyar da ya horar kafin zuwansa Arsenal.

Bayer Leverkusen za ta hadu ne da Atletico Madrid a Jamus.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.