Isa ga babban shafi
FIFA

Madrid ta lashe kofin zakarun Duniya a Morocco

Real Madrid ta lashe kofin zakarun kungiyoyin nahiyoyin duniya da aka gudanar a kasar Morocco bayan ta doke San Lorenzo ci 2-0 a ranar Assabar. Wannan shi ne kofi na hudu da Real Madrid ta lashe a 2014. Real Madrid ta buga wasanni 22 ba tare da samun galabarta ba a bana, kuma ita ke jagorancin teburin La liga a Spain.

'Yan Wasan Real Madrid suna biki a Morocco
'Yan Wasan Real Madrid suna biki a Morocco Reuters
Talla

Bayan kammala bikin lashe kofin a Morocco Cristiano Ronaldo ya nufi garin shi na haihuwa a kasar Portugal domin kaddamar da wani mutum-mutumin shi da aka girke a cikin wani gidan tarihinsa da ya ke jera kayutukan da ya lashe.

La liga.

A La liga a Spain Barcelona ta lallasa Cordoba ci 5 da 0, kuma a wasan ne Luis Suarez ya jefa kwallon shi ta farko a La liga tun zuwansa Barcelona.

Atletico Madrid kuma ta doke Bilbao ne ci 4-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.