Isa ga babban shafi
Faransa

Thierry Henry ya yi ritaya

Thierry Henry na Faransa ya bayyana yin ritaya daga buga tamola bayan shafe shekaru kusan 20 yana taka kwallo. Henry zai fara yi wa kafar Telebijin ta wasanni Sky Sport sharhi a Ingila. Henry ya aiko da sakon yin ritayarsa a shafin Facebook.

Thierry Henry sanye da rigar kungiyar Red Bulls ta New York.
Thierry Henry sanye da rigar kungiyar Red Bulls ta New York. Reuters
Talla

Henry mai shekaru 37 ya lashe wa Faransa Kofin duniya da kofin Turai, tare da lashe kofin Zakarun Turai a Barcelona.

Henry shi ne jarumin Arsenal wanda ya fi kowa yawan zirara kwallo a raga a tarihin Kungiyar, kafin ya koma Barcelona.

Henry ya kawo karshen taka kwallo ne a kungiyar New York Red Bulls ta Amurka bayan kawo karshen kwangilarsa a 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.