Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Arsenal ta doke Dortmund, Ronaldo ya yi kafada da Raul

Arsenal ta tsallake zuwa zagaye na gaba a gasar Zakarun Turai bayan ta doke Borussia Dortmund ci 2-0 a jiya Laraba. Karo na 15 ke nan a jere Arsenal na shiga zagaye na biyu a gasar, amma Dortmund ta tsallake zuwa zagaye na biyu a rukuninsu na D.

Dan wasan Arsenal Alexis Sanchez yana jefa kwallo a ragar Borussia Dortmund
Dan wasan Arsenal Alexis Sanchez yana jefa kwallo a ragar Borussia Dortmund REUTERS/Eddie Keogh
Talla

Arsenal na iya jagorantar rukunin idan ta doke Galatasaray a watan gobe, idan kuma Dortmund ta sha kashi a gun Anderlecht.

Mario Mandzukic ya jefa kwallaye uku a ragar Olympiakos wanda taimakawa Atletico Madrid doke Olympiakos ci 4-0. Kuma wannan nasarar ta ba Atletico damar tsallakewa zuwa zagaye na gaba.

Juventus ta doke Malmo ci 2-0.

Real Madrid mai rike da kofin gasar ta doke Basel ne ci 1-0 kuma Cristiano Ronaldo ne ya jefa kwallon a raga, kwallon shi ta 71 a gasar zakarun Turai wanda ya ba shi damar yin kafada da Raul.

A jiya ne Messi ya sha gaban Raul bayan ya jefa kwallaye uku wanda ya bashi jimillar kwallaye 74 a matsayin sarkin raga a gasar.

Sakamakon wasan Real Madrid dai ya taimakawa Liverpool samun kwarin gwiwar iya tsallakewa zuwa zagaye na gaba duk da ta tashi ci 2-2 da Ludogorets.

Dole sai Liverpool ta lashe wasanta na gaba a gida, kafin ta iya shiga zagaye na gaba a gasar.

Bayer Leverkusen ma ta shiga tsagaye na gaba duk da ta sha kashi a hannun Monaco ci 1-0. Bayer Leverkusen ta tsallake ne bayan Zenit ta doke Benfica ci 1-0
Monaco ta Faransa kuma na iya shiga zagaye na biyu idan ta doke Zenit.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.