Isa ga babban shafi
Premier League

Liverpool ta sha kashi, Man U ta doke Arsenal

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya dauki alhakin kashin da ya sha a karshen mako inda Crystal Palace ta lallasa Liverpool ci 3 da 1 a jiya Lahadi. Karo na uku ke nan a jere Liverpool na shan kashi a Premier League, kuma Rodgers ya sha alwashin farfado da kungiyar, domin tabbatar da makomar shi.

Raheem Sterling da Steven Gerrard na Liverpool a lokacin da suka sha kashi a hannun Crystal Palace
Raheem Sterling da Steven Gerrard na Liverpool a lokacin da suka sha kashi a hannun Crystal Palace REUTERS/Eddie Keogh
Talla

Yanzu tazarar maki 18 ne Chelsea ta ba Liverpool a teburin Premier, bayan Liverpool ta buga wasanni hudu ba nasara.

Manchester United kuma ta farfado ne zuwa matsayi na hudu a teburin Premier bayan ta doke Arsenal ci 2 da 1.

Wayne Rooney ne ya zirawa Manchester Kwallo a ragar Arsenal da ya ba United nasara a filin Emirate gidan Arsenal.

Sai dai tazarar maki 13 ne Chelsea ta ba Manchester da ke matsayi na hudu a yanzu.

Manchester City da ke matsayi na uku a teburin gasar ta doke Swansea ne ci 2 da 1 a Etihad,

A yau Litinin ne kuma Southampton da ke matsayi na biyu za ta nemi datse yawan makin da ke tsakaninta da Chelsea idan ta doke Aston Villa, bayan Chelsea ta lallasa West Brom ci 2 da 0 a ranar Assabar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.