Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Portugal ta samu sa'ar Argentina

Kasar Portugal ta samu sa'ar doke Argentina ci 1 da 0 a  wasan sada zumunci da aka kara tsakanin Cristiano Ronaldo da Lionel Messi, a filin wasa na Old Trafford na kungiyar Manchester United.

Cristiano Ronaldo na Portugal da Lionel Messi na Argentina
Cristiano Ronaldo na Portugal da Lionel Messi na Argentina eurosport
Talla

Ana dab da kammala wasa ne Portugal ta samu sa'ar zira kwallo a ragar Argentina.

Ido ya koma ne ga Messi da Ronaldo wadanda yanzu haka ke takarar lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya a bana. Amma an cire zaratan 'yan wasan bayan dawowa hutun rabin lokaci.

Duk da cewa Old Trafford gida ne ga Ranoldo amma akwai ‘Yan wasa irinsu Angel Di Maria na Argentina wanda yanzu haka ke taka kwallo a Manchester da kuma da Carlos Tevez tsohon dan wasa a Old Trafford.

Messi da Ronaldo sun karbi kyautar gwarzon dan wasan duniya a tsakaninsu sau shida.

Messi ya lashe kofin zakarun Turai guda uku a Barcelona, yayin da Ronaldo ya lashe biyu a Real Madrid da Manchester, kuma Messi yana da kofin League guda shida, yayin da kuma Ronaldo ke da uku a Real Madrid da Manchester.

Kasar Jamus ma ta samu sa'ar doke Spain ci 1-0, yayin da kuma Ingila ta doke Scotland ci 3-1 a wasan sada zumunci da kasashen suka fafata a ranar Talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.