Isa ga babban shafi
Wasanni

An zabi Amaju Pinnick a matsayin sabon shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya

Sakamakon zaben da aka yi na shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF da aka kammala cike da rudani, kuma an zabi Amaju Pinnick ne a matsayin shugaba bayan da aka soke halascin mutum mafi kwarjini a cikin ‘yan takarar wanda kuma daga yankin Arewacin kasar yake wato Shehu Dikko

sunnewsonline.com
Talla

Dama dai jiya an jinkirta gudanar da zaben ne daga karfe 10 na safiya har zuwa kusan karfe 5 na yamma.

Wannan kuwa ya faru ne sakamakon kama shugaban ‘yan kwamitin zaben da aka ce jami’an hukumar tsaron najeriya suka yi awon gaba da shi, wato chief Samson Ebomhe a dakinsa na Otal da ke a birnin Warri na jihar Delta a kudancin kasar.

To bayan da aka sako shi shugaban zaben yana zuwa aka ce sai ya bayyana cewar mutum na gaba a farin jini cikin masu takarar shugabancin hukumar wato Shehu Dikko, bai cancanta ma ya tsaya takara ba, kuma aka cire shi daga cikin ‘yan takara amma ba’a fadi dalilin rashin cancantarsa ba.

Sai dai masu lura da al’amurran yau da kullum musamman a fannin kwallon Kafa, na ganin cewar hakan bata rasa nasaba da kwadayin da wasu ke nunawa na ganin cewar ko ta halin kaka shugabancin Hukumar ya koma Kudancin kasar.

Amma fa ba a nan Gizo ke saka ba, domin ita dai FIFA ta lashi takobin cewar muddin Najeriya bata mutunta ka’idojin zaben ba, to fa za ta dakatar da kasar ga shiga sha’anin wasanni na tsawon lokaci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.