Isa ga babban shafi
Wasanni

CAF ta fitar da sunayen kasashen da za su shirya wasannin cin kofin Afirka

A ranar asabar ta makon da ya gabata ne hukumar kwallon kafa ta Afirka wato CAF ta fitar da sunayen kasashen da za su dauki nauyin shirya gasar neman kofin nahiyar na shekara ta 2019, 2021 da kuma 2023.

Tambarin CAF
Tambarin CAF REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Kasar Kamaru ce dai za ta karbi gasar ta 2019, sai Ivory coast da za ta shirya gasar a 2021 yayin da ba zato ba tsammani aka bai wa Guinea Conakry damar daukar nauyin shirya gasar ta 2023 idan Allah ya kai mu.

Akwai wasu kasashe biyu da suka bukaci samun wannan damar amma suka fadi wato Algeria da kuma Zambia, yayin da kimanin watanni 2 da suka gabata Jamhuriyar Dimokuradiyyyar Congo ta janye takararta.

Wannan ne dai karo na farko tun shekarar 1972 da kasar Kamaru ta samu damar daukar nauyin shirya wannan gasa, kuma a birane 4 na kasar ne za a buga wasannin wato Bafoussam, Douala, Garoua da kuma Yaounde.

Ivory Coast kuwa ta dauki nauyin shirya gasar karo na karshe ne a 1984, inda a shekara ta 2021 za a buga wasannin a birane 5 wato Abidjan, Bouake, Korhogo, San Pedro da kuma Youmoussoukro.

Ita kuwa kasar Gunea Conakry wadda aka bai wa wannan dama karo na farko a tarihi, za a buga wasannin ne a biranen Conakry, Kankan, Labe da kuma Nzerekore.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.