Isa ga babban shafi
Premier League

Chelsea ta doke Swansea, City ta rike Arsenal

Diego Costa ya jefawa Chelsea kwallaye uku a raga wanda ya ba Mourinho nasarar doke Swansea City ci 4 da 2 a gasar Premier ta Ingila. Manchester City kuma ta rike Arsenal ne a Emirate a fafatawar da suka yi a yau Assabar.

Dan wasan Chelsea Diego Costa yana murnar zira kwallo a ragar Swansea.
Dan wasan Chelsea Diego Costa yana murnar zira kwallo a ragar Swansea. REUTERS/Toby Melville
Talla

Ana minti 11 da fara wasa John Terry ya fara cin ragarsu wanda ya fara ba Swansea nasara a Stamford Bridge amma daga bisani Costa ya farke kwallon.

Yanzu haka Diego Costa ya jefa kwallaye bakwai a gasar Premier League tun zuwansa gasar daga La liga a Spain.

Chelsea ce ke jagorancin teburin Premier da maki 12 a wasanni hudu da aka buga a gasar.

Kungiyar Manchester City kuma ta rike Arsenal ne ci 2 da 2 a filin wasa na Emirate.

Sai a gobe Lahadi ne Manchester United zata karbi bakuncin Queens Park Rangers inda ake sa ran Van Gaal zai zuba sabbin ‘yan wasansa Radamel Falcao da Marcos Rojo da Daley Blind.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.