Isa ga babban shafi
Faransa

Ribery yana nan kan bakarsa

Franck Ribery da ke taka kwallo a Bayern Munich yace yana nan kan bakarsa na dakatar da bugawa Faransa kwallo na har abada duk da wasu rahotanni da suka ce Dan wasan yana fuskantar barazana daga shugaban kwallon Turai Michel Platini.

Franck Ribéry na Faransa da ya yi ritaya
Franck Ribéry na Faransa da ya yi ritaya REUTERS/Charles Platiau
Talla

Wasu Jaridu a Faransa da Jamus ne suka ruwaito cewa Platini ya yi gargadin dakatar da Ribery idan har ya ki bugawa kasar shi wasa idan aka nemi ya bugawa Faransa kwallo. Amma dan wasan yace yana nan kan bakarsa.

Wannan na zuwa ne a yayin da Shugaban Faransa Francois Hollande a yau ya yi alkawalin cewa Faransa zata gudanar da gasar cin kofin Turai da ba za’a taba mantawa ba a 2016.

Shugaban kuma ya fadi haka ne a lokacin kaddamar aikin karbar bakuncin gasar a fadarsa tare da shugabannin kwallon kafa na Turai da kuma Ministocinsa da Magadan gari.

Hollande yace dama ce Faransa ta samu na inganta kwallon kafa da kuma biranenta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.