Isa ga babban shafi
Najeriya

An dakatar da Premier a Najeriya

A Najeriya an dakatar da wasannin league din kasar saboda yajin aikin da alakalan wasanni suka shiga sakamakon rikicin da ya daibaidaiye hukumar wasannin. Kwamitin shirya wasannin na Premier a Najeriya yace sun dakatar da wasannin kamar yadda kungiyar alkalan wasa ta bukata.

Tambarin gasar Premier a Najeriya
Tambarin gasar Premier a Najeriya Wikipedia
Talla

Tun watan Yuli hukumar kwallon Nagerita NFF ta fada cikin rikici bayan kammala gasar cin kofin Duniya, lamarin da yasa FIFA ta dakatar da Najeriya kafin daga bisani ta dage matakin.

Kungiyar alkalan wasan ta bukaci mambobinta su kauracewa alkalancin wasannin Premier har sai an tsabtace wasannin.

A yau Juma’a Kungiyar ‘Yan wasa da masu horar da ‘Yan wasa sun kauracewa wasannin na Premier har sai baba ta gani

Tuni dai aka yi nisa da wasannin Premier a Najeriya, domin ana mako na 25 a wasannin, inda Kano Pillers ke jagorancin Tebur da maki 43.

Hukumar kwallon duniya FIFA na iya sake daukar mataki akan Najeriya saboda rikicin siyasar hukumar NFF.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.