Isa ga babban shafi
Najeriya

An saki Maigari

'Yan Sandan Farin kaya na SSS a Najeriya sun saki Alhaji Aminu Maigari shugaban hukumar kwallon Najeriya mai murabus bayan cafke shi a lokacin da suke shirin gudanar da taron hukumar na kasa domin shirya zaben wanda zai maye gurbinsa a Abuja.

Shugaban hukumar kwallon Najeriya Aminu Maigari
Shugaban hukumar kwallon Najeriya Aminu Maigari Kickoff.com
Talla

An dai cafke Maigari ne tare da sakataren hukumar NFF Musa Amadu, amma daga bisani an saki Amadu, wanda kuma ya jagoranci taron sauran mambobi 44 da suka kunshi shugabannin hukumar na jahohi da suka tsayar da ranar 4 ga watan Satumba da za’a gudanar da sabon zaben sabbin shugabanni.

Bangare guda kuma da suka ware sun zabi Chris Giwa a matsayin sabon Shugaban hukumar bayan sun jefa kuri’a a Chida Hotel a Abuja, tare da ba sauran mambobin taron na ‘Yan tawaye mukamai da dama.

Bangaren Maigari dai sun yi watsi da zaben, kuma an gudanar da zaben ne ba tare da wakilin hukumar FIFA ba da ke kula da sha’anin kwallo a duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.