Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Ginin hukumar NFF a Nigeria ya ci wuta

Hukumar kwallon kafa ta kasa a Nigeria NFF, da ke fama da rikce rikice ta sake samun wata matsalar yau laraba, don shalkwatar hukumar, da ke Unguwar Wuse zone 7 ta ci wuta. Ginin hukumar, da ake kira Glass House mai hawa 2 ya fara cin wuta ne daga sama, kuma wutar ta warwatsu, kafin ‘yan kwana kwana su isa wurin.Har yanzu ba a san musabbabin wutar ba.Dama hukumar ta NFF na fama da rikice rikice tsawon watanni, inda hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar da ita a watan Yulin daya gabata, kan abinda ta kira katsalandan daga hukumomin kasar.Matakin da FIFA ta dauka yazo ne bayan wata kotun kasar ta kori shugabannin hukumar ta NFF, karkashin Aminu Maigari, kuma gwamnati ta nada kantoma a Hukumar. 

Jami'an kiyaye hadari suna kokarin kashe wuta a ginin hukumar Kwallon Najeriya NFF
Jami'an kiyaye hadari suna kokarin kashe wuta a ginin hukumar Kwallon Najeriya NFF REUTERS/Afolabi Sotunde
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.