Isa ga babban shafi
Champions League

Arsenal ta rike Besiktas a Istanbul

Kungiyar Arsenal ta rike Besiktas ta Turkiya babu ci a gidanta, a karawa ta farko da suka fafata a Intanbul, a wasannin neman shiga gasar zakarun Turai da kungiyoyin biyu fafata a jiya Talata.

Dan wasan Arsenal Aaron Ramsey  yana ficewa fili bayan ya karbi jan kati a fafatawarsu da Besiktas ta Turkiya
Dan wasan Arsenal Aaron Ramsey yana ficewa fili bayan ya karbi jan kati a fafatawarsu da Besiktas ta Turkiya REUTERS/Murad Sezer
Talla

Arsene Wenger kocin Arsenal ya caccaki alkalin wasa bayan ya ba dan wasansa Ramsey jan kati ana saura minti 10 a kammala wasan.

Sau 12 Arsenal na samun nasara a wasanninta na neman shiga gasar cin kofin zakarun Turai, amma akwai babban kalubale a gabanta a bana inda dole sai ta nemi nasara a akrawa ta biyu.

Bayer Leverkusen ta Jamus kuma ta bi FC Copenhagen har gida ta doke ta ci 3 da 2.
Steaua Bucharest ta Romalnia ta doke Ludogorets ta Bulgeria ci 1 da 0.

Napoli da Athletic Bilbao sun yi kunnen doki ne ci 1 da 1

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.