Isa ga babban shafi
Scotland

Wasannin renon Ingila a rana ta Bakwai

A yau Laraba aka shiga rana ta bakwai a wasannin kasashen renon Ingila da ake gudanarwa a birnin Glasgow a kasar Scotland, inda a yau za’a fafata a tseren gudun mita 400 a bangaren Maza da mata. Kasar Australia ce ke kan gaba da yawan zinari da jimillar lambobin yabo 101, yayin da Ingila ke bi mata da jimilla 93.

Brianne Theisen-Eaton  ta Canada ta sha gaban 'yar uwarta Jessica Zelinka a tseren gudun mita 200 a wasannin kasashen renon ingila da ake gudanarwa a Scotland
Brianne Theisen-Eaton ta Canada ta sha gaban 'yar uwarta Jessica Zelinka a tseren gudun mita 200 a wasannin kasashen renon ingila da ake gudanarwa a Scotland REUTERS
Talla

Kasar Canada ce matsayi na uku.

Kasar Afrika ta kudu ce a sahun gaba a Kasashen Afrika da ke haskawa a wasannin, amma ta bakwai da yawan lambobin yabo 26 a jerin kasashen renon Ingila da ke fafatawa.

Kasar Kenya tana matsayi na 10 da yawan lambobin yabo 9. Najeriya tana matsayi na 12 ne, da yawan zinariya 6 tagulla uku, azurfa 5, jimilla 14.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.