Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

‘Yan wasa suna kauracewa Ukraine

Wasu ‘Yan wasan kwallon kafa guda uku sun kauracewa kungiyar Volyn Lutsk ta Ukraine cikinsu har da Dan Najeriya, saboda kazamin rikicin da ake yi a gabacin kasar. ‘Yan wasan sun hada da Dan kasar Romania Eric Bicfalvi da Ramon Lopes na Brazil da Michel Babatunde na Najeriya, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Magoya bayan kungiyar Shakhtar Donetsk a Ukraine
Magoya bayan kungiyar Shakhtar Donetsk a Ukraine REUTERS/Gleb Garanich
Talla

A makon jiya kusan ‘Yan wasa guda bakwai ne suka kauracewa kungiyar Shakhtar Donetsk bayan harbo jirgin Malaysia a gabacin Ukraine.

Yanzu haka rahotanni sun ce ‘Yan wasa da dama ne na kasashen waje da ke buga kwallo a Ukraine ke son ficewa daga kasar saboda rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.