Isa ga babban shafi
Wasanni

Bukin buda wasannin kasashe renon Ingila a wannan laraba

A wannan laraba ne za a buda wasannin kasashen kungiyar Commenwealth wato kasashe renon Ingila wasannin da za su gudana a birnin Glasgow na kasar Scotland.

Tambarin wasannin Commonwealth
Tambarin wasannin Commonwealth
Talla

Wannan ne dai karo na 20 a tarihi da za a gudanar da wannan gasa wadda ta samo asali tun shekarar 1930.

A bana dai akwai ‘yan wasa akalla dubu 4 da 500 da za su shiga gasar, kuma sun fito ne daga kasashen duniya 71 mambobi a wannan kungiya ta Commonwealth.

Bayan buda wannan gasa a yau, gobe alhamis za a soma fafata gadan-gadan.

To wani abin tuni a nan shi ne, a shekarar ta 2007 ne a kasar Sri Lanka aka jefa kuri’ar da ke bai wa birnin na Glasgow damar daukar nauyin gasar, bayan da ya doke birnin Abuja na tarayyar Najeriya da kuri’u 47 a kan 24.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.