Forbes: Real da Barca sun fi kudi
Mujallar Forbes ta fitar da jerin attajiran kungiyoyin kwallon wasanni a Duniya, kuma manyan kungiyoyin kwallon kafa na Spain ne guda biyu Real Madrid da Barcelona aka bayyana a sahun gaba.
Wallafawa ranar:
Karo biyu a jere, Real Madrid ce ta daya da arzikin kudi dalar Amurka biliyan 3.44.
Barcelona ce a matsayi na biyu da arzikin kudi Dala Biliyan 3.2. Sai Manchester United a Ingila a matsayi na uku da arzikin kudi dala Biliyan 2.81.
A cikin jerin kungiyoyi guda 10 masu arziki akwai kungiyar kwallon kafa Bayern Munich ta Jamus a matsayi na bakwai amma sauran sun kunshi kungiyoyin Baseball da kwallon zari ruga.
Kungiyoyi 10 masu arziki.
1. Real Madrid $3.44 billion
2. Barcelona $3.2 billion
3. Manchester United $2.81 billion
4. New York Yankees $2.5 billion
5. Dallas Cowboys $2.3 billion
6. Los Angeles Dodgers $2.0 billion
7. Bayern Munich $1.85 billion
8. New England Patriots $1.8 billion
9. Washington Redskins $1.7 billion
10. New York Giants $1.55 billion.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu