Isa ga babban shafi
Ingila

Hannayen Jarin Manchester sun tashi bayan sallamar Moyes

Hannayen jarin kungiyar Manchester United sun tashi sama da kusan kashi 6 a jiya talata bayan sallamar mai horar da ‘Yan wasan kungiyar David Moyes. Jaridar The Time a Birtaniya ta ruwaito cewa Sir Alex Ferguson ya goyi bayan matakin da Manchester ta dauka na korar Moyes da ya gaje shi.

David Moyes da Manchester United ta kora.
David Moyes da Manchester United ta kora. REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

Alkalumman hannun jarin Manchester shi ne aka bayyana mafi kyau tun a ranar biyu ga watan Mayun bara, tun da Sir Alex Ferguson ya fice kungiyar wanda David Moyes ya gada.

A karkashin jagorancin David Moyes, Manchester United da ta lashe kofin Premier a bara, a bana tana matsayi na bakwai ne a Teburin Premiership, yayin da kuma aka yi waje da ita a sauran gasannin cikin gida da gasar zakarun Turai.

Jaridar The Time ta ruwaito cewa Sir Alex Ferguson ya bayyana goyon bayansa ga matakin sallamar David Moyes, wanda shi da kansa ne ya zabo shi, bayan ya yi ritaya.

Kuma Jaridar tace duk da Ferguson ya zabarwa United makoma marar kyau amma za’a sake tuntubarsa domin bayar da shawara akan wanda ya dace da aikin horar da ‘Yan wasan Kungiyar.

Wasu manyan Jaridun Birtaniya a yau Laraba sun ruwaito cewa Carlo Ancelotti na Real Madrid ya shiga cikin sahun masu horar da ‘Yan wasan da Manchester ke son dauka, duk da yanzu dan wasan Kungiyar Ryan Giggs ne aka ba jagoranci na wuccin gadi.

Sai dai kuma har yanzu Jaridun, sun fi mayar da hankali ne akan kocin kasar Netherlands Louis Van Gaal a matsayin wanda ke sahun gaba.

Jaridar the Sun tace Manchester ta fara tunanin Ancelotti ne saboda akwai sabani tsakanin shi da shugabannin kungiyar Real Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.