Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Guardiola ya kariya da Real Madrid

Pep Guardiola mai horar da ‘Yan wasan Kungiyar Bayern Munich ya bayyana damuwa kafin haduwar shi da Real Madrid a gasar zakarun Turai bayan ya sha kashi a jere da jere a gasar Bundesliga ta Jamus.

Josep Guardiola mai horar da 'Yan wasan Bayern Munich
Josep Guardiola mai horar da 'Yan wasan Bayern Munich ©Reuters
Talla

Guardiola yace idan ‘yan wasan shi zasu yi wasa kamar yadda suka yi a wasanni uku da suka gabata a Bundesliga, yana ganin ba za su iya tsallakewa zuwa birnin Lisbon da za’a yi fafatawar karshe a gasar zakarun Turai.

A yau ne Bayern Munich zata kara da Kaiserslautern a gasar lashe kofin Jamus tare da fatar samun nasara domin sake haduwa da Borussia Dortmund da ta lallasa ta a Bundesliga a karshen mako.

Tun lokacin da Bayern Munich ta lashe kofin Bundesliga makwanni biyu da suka gabata, nasara guda Guardiola ya samu a wasanni biyar da suka gabata.

A bana Bayern Munich na fatar kafa tarihi ne a matsayin kungiya ta farko da zata kare kofin zakarun Turai a tarihi bayan ta lashe kofin a bara da kofin Bundesliga da kofin gida na Jamus da kofin Super da kofin zakarun kungiyoyin duniya.

Guardiola ya amsa cewa suna cikin tsaka mai wuya, kuma babban kalubalae da ya fuskanta tun lokacin da ya karbi aikin horar da kungiyar Bayarn Munich bayan ya fito daga Barcelona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.