Isa ga babban shafi
Premier League

Yaya Toure ya tafi jinya

Yaya Toure na Manchester City zai kwashe lokaci yana jinya saboda raunin da ya samu a karawar da Liverpool ta doke su ci 3-2 a gidanta. Kocin City Maneul Pellgrini yace duk da sun sha kashi a hannun Liverpool amma yana da yakinin zasu iya lashe kofin gasar idan har suka samu nasara ga kwanten wasanninsu guda biyu.

Yaya Touré na  Manchester City.
Yaya Touré na Manchester City. REUTERS/Nigel Roddis
Talla

Tazarar maki 7 ne Liverpool ta ba Manchester city da ke matsayi na uku. Maki biyu ne ya raba Liverpool da Chelsea da ke matsayi na biyu wacce ta sha da kyar da hannun Swansea ci 1-0.

Liverpool tana harin lashe kofin Premier ne a karon farko tsawon shekaru sama da 20 da suka gabata, kodayake wasanni hudu suka rage, kuma cikin wasannin, Liverpool zata kara da Chelsea a Stamford Bridge.

Steven Gerard sai da ya barke da kuka saboda jin dadin nasarar da suka samu akan Manchester City

Kofin FA.

Kungiyar Arsenal na iya kawo karshen yunwar kofin da ta ke yi na tsawon shekaru 9 bayan ta tsallake zuwa buga wasan karshe a gasar FA.

Arsenal ta doke Wigan ne a wasan dab da na karshe kuma yanzu zata hadu ne da Hull City a filin wasa na Wembley a ranar 17 ga watan Mayu, inda Hull ke harin lashe kofin gasar a karon farko tsawon shekaru 110 na tarihin gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.