Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Earopa League: Valencia da Sevilla sun sha

Kungiyoyin Spain guda biyu Sevilla da Valencia da dukkaninsu sun tsallake zuwa zagayen dab da na karshe a gasar Europa League bayan sun samu nasarar wasanninsu. Sevilla da Valencia sun rama kashin da suka sha ne a karawa ta farko inda a daren Alhamis Sevilla ta lallasa FC Porto ci 4-1, bayan ta sha kashi ci 1-0 a karawa ta farko.

'Yan wasan Kungiyar Valencia a Spain
'Yan wasan Kungiyar Valencia a Spain REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Valencia kuma ta doke Basel ne ci 5-0 bayan ta sha kashi ci 3-0 a karawa ta farko.
Juventus ta yi waje da Lyon da jimillar kwallaye ci 3-1 bayan ta doke ta ci 2-1 a daren jiya.

A yau Juma’a ne za’a kungiyoyin da zasu kara da juna a gasar Europa league a zagayen dab da na karshe, tare da kungiyoyin da zasu kara a gasar Zakarun Turai, tsakanin Bayern Munich mai rike da kofin gasar da Real Madrid da ke harin lashe kofin gasar karo na 10 da kuma Chelsea da Atletico Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.