Isa ga babban shafi
Champions League

Bayern da Atletico sun yi waje da Manchester da Barca

A karon farko bayan shafe shekaru 40, kungiyar Atletico Madrid ta tsallake zuwa zagayen dab da na karshe a gasar zakarun Turai bayan ta yi waje da Barcelona da jimillar kwallaye ci 2-1. A Filin wasa na Allianz Arena a Jamus, Kungiyar Bayern Munich kuma ta yi waje ne da Manchester United da jimillar kwallaye ci 4-2.

Mai horar da 'Yan wasan Bayern Munich Pep Guardiola yana jinjinawa Arjen Robben bayan ya zira kwallo a ragar Manchester United a gasar zakarun Turai
Mai horar da 'Yan wasan Bayern Munich Pep Guardiola yana jinjinawa Arjen Robben bayan ya zira kwallo a ragar Manchester United a gasar zakarun Turai REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

Tun da fara wasa ne Koke ya zira wa Atletico Madrid kwallo a raga, yayin da David Villa ya daki karfen ragar Barcelona har sau biyu.

Shekaru hudu rabon da Atletico ta samu galabar Barcelona, kuma yanzu Atletico ita ce ke jagorancin teburin La liga.

Yanzu kungiyoyin Spain guda biyu ne ‘yan gari guda suka tsallake zagayen dab da na karshe, Atletico da Real Madrid, inda wannan ne karo na biyu da kungiyoyin guda biyu suka tsallake bayan sun tsallake a 1959.

Lionel Messi na Barcelona ya dafe kai bayan sun sha kashi a hannun Atletico Madrid
Lionel Messi na Barcelona ya dafe kai bayan sun sha kashi a hannun Atletico Madrid REUTERS/Juan Medina

Bayern Munich kuma na neman zama kungiya ta farko da ke harin kare kambunta bayan ta lashe kofin gasar zakarun Turai a bara.

Yanzu Altetico Madrid da Bayern Munich sun bi sahun Chelsea da ta yi waje da PSG da kuma Real Madrid da ta yi waje da Borussia Dortmund, inda za’a hada Kungiyoyin wasa a gobe Juma’a domin fafatawa a zagayen dab da na karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.