Isa ga babban shafi
Tennis

French Open: Nadal da Djokovic za su iya haduwa a zagayen kusa da karshe

Kafin gudanar da gasar Franch Open ta Rolland Garros a karshen mako, rukunin ‘yan wasan da aka hada ya nuna zaratan ‘Yan wasan Tennis na duniya, Novak Djokovic da kuma Rafael Nadal na uku wanda ke harin lashe kofin gasar karo na 8, suna iya haduwa a wasan dab da na karshe.

Tambarin gasar Rolland Garros
Tambarin gasar Rolland Garros Flickr
Talla

Roger Federer, na iya tsallakewa zuwa zagayen karshe ba tare da ya kara da Nadal ba ko Novak Djokovic.

A bara Rafeal Nadal da Novak Djokovic, ne suka fafata a wasan karshe, amma Nadal ya haramtawa Djokovic, lashe babbar gasar da har yanzu ya ke farautar lashewa cikin jerin kufunan da ya lashe na Australian Open da US Open da kuma Wimbledon.

A ranar Lahadi ne dai za’a fara kece raini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.