Isa ga babban shafi
Spain

Messi yana fama da zazzabi

Likitan kungiyar Barcelona ya ce Lionel Messi yana fama da zazzabi wanda ya sa dan wasan ya kauracewa horo a tawagar kungiyar bayan sun sha kashi a gida hannun Real Madrid a gasar Copa Del Ray.

Dan wasan Barcelona Lionel Messi
Dan wasan Barcelona Lionel Messi
Talla

“Dan wasan kasar Argentina yana fama da zazzabi”, a cewar shafin Intanet na Barcelona bayan likitan kungiyar ya kai ziyar gidansa domin duba lafiyar dan wasan.

Messi yana cikin tawagar Barcelona da suka sha kashi ci 1-3 hannun Real Madrid a gasar Copa Del Ray.

Kungiyar Barcelona tana fatar dan wasan zai murmuje kafin ranar Assabar domin sake karawa da Real Madrid a La liga.

“Tawagar ‘Yan wasan Barcelona za su tafi hutu a ranar Alhamis amma muna fatar (Messi) mai lamba 10 zai fito horo a ranar Juma’a, ranar karshe kafin karawa da Real Madrid a Bernabeu," a cewar Shafin intanet na Barcelona

Tazarar maki 16 ne a bana Barcelona ta ba Real Madrid a teburin La liga, kuma Messi ya haska a dukkanin wasannin Barcelona da kungiyar ta buga a gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.