Kwallon Kafa - 
Wallafa labari : Laraba 12 Satumba 2012 - Bugawa ta karshe : Laraba 12 Satumba 2012

Lampard ya ceto Ingila, Van Persie ya samu rauni

Dan wasan Holland Robin van Persie  a lokacin da ya samu rauni a wasa neman shiga gasar cin kofin Duniya tsakanin Holland da Hungary
Dan wasan Holland Robin van Persie a lokacin da ya samu rauni a wasa neman shiga gasar cin kofin Duniya tsakanin Holland da Hungary
REUTERS/Laszlo Balogh

Daga Awwal Ahmad Janyau

A wasannin neman shiga gasar cin kofin Duniya da aka gudanar a jiya Talata a kasashen Turai, a filin wasa na Wembley, wasa tsakanin Ingila da Ukraine an tashi ne kunnen doki ci 1-1 kuma Frank Lampard ne ya taimakawa Ingila zira kwallo a raga, sai dai kafin kammala wasan alkalin wasa ya ba Steven Gerrard jan kati.

Kasar Italia kuma ta lashe wasanta na farko a fafatawar neman shiga gasar cin kofin Duniya, inda a jiya ta doke Malta ci 2-0 a birnin Modena. Mattia Destro da Federico Peluso ne suka zirawa Italia kwallayenta a raga.

Dan wasan Valencia ne kuma Roberto Saldado ya taimakawa Spain doke Georgia ci 1-0.

Kasar Belarus kuma tasha kashi ne hannun Faransa ci 3-1.

Kasar Holland kuma ta doke Hungary ci 4-1 a birnin Budapest. Sai dai dan wasan Manchester United Robin Van Persie bai sha da dadi ba domin ya fice wasan saboda rauni.

Kasar Romania ta doke Andorra ne ci 3-0. Kamar yadda kasar Jamus ta lallasa Austria ci 2-1. Marco Reus da Mesut Ozil su ne suka zirawa kasar Jamus kwallayenta biyu a raga. Yayin da kuma Zlatko Junuzovic ya zira wa Austria kwallonta daya a ragar Jamus
A birnin Istanbul kuma kasar Turkiya ta lallasa Estonia ci 3-0. Kasar Rasha kuma ta doke Isra’ila ci 4-0.

Kasar Azerbaijan kuma ta sha kashi ne hannun Portugal ci 3-0.
 

tags: Gasar Cin Kofin Duniya - Kwallon Kafa - Wasanni
KAN MAUDU'I GUDA
Ra'ayoyi
Bada ra'ayi kan wannan magana
The content of this field is kept private and will not be shown publicly.
To prevent automated spam submissions leave this field empty.
CAPTCHA
This question is for testing whether you are a human visitor and to prevent automated spam submissions.
Close