Isa ga babban shafi
FIFA

Sudan ta Kudu ta samu shiga jerin matsayi na FIFA

A karon farko Sudan ta Kudu ta shiga jerin ajin matsayi na hukumar FIFA da ke kula da kwallon kafa a duniya bayan buga wasan farko a watan jiya. Kodayake an tashi wasan ci 2-2 ne da kasar Uganda amma Sudan ta Kudu ita ce a matsayi na 199 cikin jerin kasashe 209 a duniya, bayan samun ‘Yancin kai a bara.

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir UN Photo/Isaac Billy
Talla

Har yanzu dai kasar Spain ce a matsayi na farko sai Jamus da ke bi mata amma yanzu Ingila ce a matsayi na uku Uruguay kuma a matsayi na 4.

A sabon jerin ajin matsayin dai Brazil ta fice daga sahun kasashe 10 a duniya inda ta koma a matsayi na 12.

1. (1) Spain
2. (2) Jamus
3. (4) Ingila
4. (3) Uruguay
5. (5) Portugal
6. (6) Italiya
7. (7) Argentina
8. (8) Netherlands
9. (9) Croatia
10. (10) Denmark
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.