Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

AC Milan ta sha kashi hannun Madrid, Barcelona ta doke Manchester

Kungiyar Real Madrid ta lallasa AC Milan ci 5-1 a wasan sada Zumunci na share fagen kakar wasa da kungiyoyin biyu suka buga a filin wasa na Yankee da ke kasar Amurka. Wasa tsakanin Barcelona da Manchester kuma an tashi ne babu ci amma Barcelona ta lashe wasan a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Dan Wasan AC milan Robinho yana gaisawa da Ronaldo a filin wasa na Yankee a kasar Amurka
Dan Wasan AC milan Robinho yana gaisawa da Ronaldo a filin wasa na Yankee a kasar Amurka REUTERS/Adam Hunge
Talla

Angel di Maria da Cristiano Ronaldo da Jose Callejon ne suka zirawa Madrid kwallayenta a ragar AC Milan .

A daya bangaren kuma wasa tsakanin Manchester United da Barcelona da aka gudanar a Gothenburg an tashi ne babu ci. Sai dai Barcelona ce ta lashe wasan ci 2-0 a bugun daga kai sai mai tsaron gida Bayan Nani da Ashley Young sun barar da Penalty.

Bayan kammala wasa ne Sir Alex Ferguson yace kudirin Manchester United na sayen Robin van Persie daga Arsenal ya mutu. Bayan dan wasan ya ki amincewa ya sabunta kwangilar shi da Arsenal.

A cewar Farguson, Manchester ta yi iya kokarinta domin mallakar dan wasan amma Arsenal bata bukatar dan wasan ya zo Manchester.

Farguson yace tun a ranar 20 ga watan yuli ne Machester ta mika bukatar sayen dan wasan ga Arsenal.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.